Fargabar Zanga Zanga: Ganduje Ya Gana da Ciyamomi APC a Jihohi, Bayanai Sun Fito

May 2024 ยท 2 minute read

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya yi wata ganawa da shugabannin APC a jihohi 36 a kasar.

Ganawar ba ta rasa nasaba da shirin zanga-zanga a fadin kasar da matasa suka shirya saboda mawuyacin hali da ake ciki.

Kara karanta wannan

"Ba mu san dalilinku ba:" Gwamnonin APC sun tura sako ga matasa kan zanga-zanga

Musabbabin ganawar Ganduje da ciyamomin APC

Sakataren jam'iyyar ta kasa, Felix Morka shi ya tabbatar da haka a jiya Juma'a 26 ga watan Yulin 2024, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje wanda ya jagoranci ganawar ya bukaci ciyamomin su zauna da gwamnonin jihohi musamman na APC domin dakile zanga-zangar.

Yayin ganawar, jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa ana shan wahala a kasar tare da nuna damuwa musamman irin halin da ake ciki.

Sakataren jam'iyyar ya ce akwai wadansu da ke son kawo rigima a zanga-zangar wadanda ba a san ko su waye ba ne, Daily Trust ta tattaro.

Zanga-zanga: Shawara da aka ba ciyamomin APC

"Yayin ganawar mun yi duba zuwa ga halin da ake ciki da kuma shirin zanga-zanga da za a fara a ranar 1 ga watan Agustan 2024."

Kara karanta wannan

Gwamnonin jihohi 36 sun yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi

"Tabbas ana cikin wani hali a Najeriya duk da haka muna tare da Bola Tinubu wurin shawo kan matalolin da ake fuskanta a kasar."Gwamnati tana iya bakin kokarinta wurin samar da sauki ga 'yan kasa yayin da wasu ke kokarin kawo rigima."

- Felix Morka

'Yan sanda sun gindaya sharuda ga masu zanga-zanga

A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta ba da damar yin zanga-zanga amma ta kasance cikin lumana ba tashin hankali.

Daga cikin sharudan shi ne shugabannin zanga-zangar su ba da bayanansu ga kwamishinonin 'yan sanda da ke jihohinsu daban-daban.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoNxgJVqcGaekae0oq7Aq2SzmZ6crm7GwKeemmWklnq0rYygmKecpZ%2BybrPAp5iwmV2Zrm6vyLKYpqednnqivMJmpZplmp61sLTIZpmasZGjrqp50q6lZp6Zqbxw